News
Magidanci Ya Yi Karar Matarsa Kan Kara Aure A Sirrance
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Wani dan kasuwa a Abuja ya maka matarsa a gaban kotu sakamakon zarginta da auren wani mutum a boye alhali akwai igiyar aurensa a tare da ita.
Magidancin ya ce matar ta sa ta bar gidansa ne ba tare da neman izininsa ba tun a shekarar 2020, sai daga bisani ya gano ta a wata unguwar ta yi aure har ta haihu.
Akwai fargabar fasinjoji sun rasu yayin da babbar mota ta murƙushe adaidaita-sahu a Kano
“Kan wannan ne nake neman kotu ta raba aure na da ita, ta kuma bani rikon ’ya’yanmu uku da ta tafi ta bar ni da su.
“Ni nake kula da su, kuma ba na so wani ya gurbata min tunaninsu a kaina, don haka ina rokon kotu ta hana matata zuwa wajensu idan ba na gida,” in ji shi.
Alkalin kotun mai shari’a Labaran Gusau ya dage shari’ar zuwa ranar 9 ga watan Fabrairu.
-
News3 days ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion6 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News2 days ago
Zaben 2027: INEC Ta Amince Da Atiku Abubakar, ‘Yan Takarar ADC 470
