Connect with us

Politics

Kwankwaso Ba Zai Goyi Bayan Kowa Ba —NNPP

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

Advertisement

 

Jam’iyyar NNPP ta musanta cewa dan takararta na shugaban kasa, Rabiu Musa Kwankwaso na tattaunawa da takwaransa na PDP, Atiku Abubakar kan goya wa takararsa baya a zaben da ke tafe.

Advertisement

 

Jam’iyyar ta bayyana haka ne ta bakin mai magana da yawun kwamitin yakin neman zabenta, Ladipo Johnson a ranar Laraba a Abuja.

Advertisement

’Yan Ta’adda Sun Kashe Sojoji 11 A Syria

 

Johnson ya ce a bayyane yake cewa Kwankwaso ya fi Atiku farin jini da kuma iya salon neman mulki.

Advertisement

 

Ya ce, wannan ya nuna Atiku na neman inda zai rabe, ganin cewa ba zai iya cin zabe ba.

Advertisement

 

 

Advertisement

Ya ce sanarwar na da matukar muhimmanci saboda Atiku ya ce dan takarar nasu na tattaunawa da shi don duba yiwuwar yadda zai mara masa baya.

 

Advertisement

“Magana ta gaskiya ita ce babu wani lokaci da aka yi wata tattaunawa tsakanin Atiku da Kwankwaso, ko kuma wasu daga cikin wakilansu.

 

Advertisement

“Sau daya suka hadu, lokacin taron ’yan takara a baya.

 

Advertisement

“Idan ’yan Najeriya ba su manta ba a baya cewa ake yi Kwankwaso ba shi da wani tasiri sai a Kano.

 

Advertisement

 

Mun shigo wannan tafiya ne don sauya yanayin da Najeriya ke ciki, don mu inganta tare da ceto mutane daga halin kunci.

Advertisement

 

 

Advertisement

 

“Abokan hamayya sun ga irin tsarin tafiyar Kwankwaso da yadda mutane ke mararin zabar sa saboda tsari da tanadi da ya zo wa da ’yan Najeriya, shi ya sa kowa ke son zabar NNPP,” in ji shi.

Advertisement

 

Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP ya bayyana cewa yana tattaunawa da Kwankwaso da Obi don ganin wani daga cikinsu ya mara wa tafiyarsa baya.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending