Connect with us

News

Dan Sanda Ya Kashe Soja A Ogun

Published

on

Rundunar Soja ta ce fusatattun matasa ne suka banka wa ofishin ‘yan sanda wuta amma ba jami’anta ba

Sojoji sun koma ofishin ’yan sanda da ke yankin Ogijo a Jihar Ogun kan zargin kashe wani abokin aikinsu da wani dan sanda ya yi da wuka.

Advertisement

Shugaba Buhari zai tafi taron Tarayyar Afirka a Ethiopia

Bayanai sun ce sojoji sun kai harin tare da banka wa ofishin ’yan sandan wuta ne sanye da kaki ba tare da sunayensu a jikin kakin ba.

Rahotanni sun ce lamarin dai ya haifar da rudani a tsakanin jama’ar yankin na tsawon sama da sa’a guda da sojojin suka ci karensu babu babbaka.

Advertisement

Majiya daga ’yan sanda ta ce sojojin da lamarin ya shafa sun fito ne daga Bataliya ta 174 a yankin Ikorodu, Jihar Legas.

Ta kara da cewa sun kai samamen ne don daukar fansa kan abin da wani dan sanda ya aikata wa abokin aikinsu.

Advertisement

Ana zargin dan sandan da ne da daba wa sojan wuka a kirji saboda sa-in-sar da ta shiga tsakaninsu.

Lamarin da ya fusata abokan aikin marigayin, inda suka bi sawun dan sandan wanda ya tsere tare da neman mafaka a ofishin ’yan sanda na Ogijo.

Advertisement

Da yake tofa albarkacin bakinsa kan lamarin ta shafinsa na Twitter, jami’in hulda da jama’a na ’yan sandan Jihar Legas, Benjamin Hundeyin, ya ce, “Muna sanar da jama’a cewa lamarin ya faru ne a Ogijo, Jihar Ogun, wanda ke kusa da Ikorodu a Jihar Legas.”

A nata martanin, Rundunar Sojojin Najeriya ta ce, “Fusatattun matasa da suka shaida abin da ya faru ne suka yi amfani da wannan dama wajen kai wa ofishin ’yan sandan hari.”

Advertisement

Hakan na kunshe ne cikin sanarwar da rundunar ta fitar a ranar Alhamis dauke da sa hannun Mataimakin Darakatan Hulda da Jama’a, na Runduna ta 81, Laftanar-Kanar Olabisi Ayeni.

Ya ce sojoji sun tsare wanda ake zargi don kare rayuwarsa tare da mika shi ga ’yan sanda domin bincike.

Advertisement

Bayan faruwar lamarin “An garzaya da sojan Asibitin Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Legas da ke Odogunyan inda aka tabbatar da mutuwarsa.

“Kuma an dauki gawar zuwa Cibiyar Kiwon Lafiya ta Bataliya ta 174 da ke Ikorodu,” in ji jami’in.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending