News
GWAMNATIN KANO TA KADDAMAR DA SHARIN BAYAR DA MAGUNGUN KYAUTA A JAHAR.
Gwamnatin jahar kano karkashin jagorancin Dakta Abdullahi Umar Ganduje ta bayar da tallafin magungun kyauta ga mata masu yuna biyu a fadin kananan hukumomi 44 da ke jahar.
Kwamishinan Lafiya na jihar kano Dakta Aminu Ibrahim Tsanyawa ne yakaddamar da Shirin na bada magungun kyauta a asibitin yara na Isyaka rabiu dake kano
INEC Ta Fara Raba Muhimman Kayan Zabe A Kananan Hukumomin Yobe
Dakta tsanyawa yace Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kano ta samar da E National Action Plan for Health Security (NAPHS) cikin tsarin samar da tsaro na Jihar Kano (KSAPHS), Kano ce jiha ta farko da ta samu wannan matsayi a fadin kasar nan. NCDC ta yabawa jihar Kano bisa samar da wannan sharin kuma ta yi kira ga sauran jihohin da su yi koyi da su.
Sauran ayyukan sun hada da raba gidajen sauro na maganin kwari kyauta ga yara da mata masu juna biyu a matsayin daya daga cikin ingantattun dabarun yaki da zazzabin cizon sauro, ayyukan tsarin iyali, rigakafi da yara kanana
Ina kuma son in yaba da gagarumar gudunmawa da goyon bayan da muke samu daga abokan aikinmu na ci gaba, irin su WHO, UNICEF, Alive & Thrive, CHAI, CO-GROUP, BMGF, LISDEL, Lafiya Project, NCDC, E Health Africa, AFENET, NPHCDA Nutrition Internal , Dangote Foundation da yawa da yawa ba a ambata ba. I na kuma mika godiyata ga abokanmu ‘yan jaridu da dukkan kafafen yada labarai bisa irin gagarumin goyon bayan da ake baiwa ma’aikatar da gwamnati.
