News
Da Dumi-Dumi: Shugabar Karamar Hukuma Ta Rasu Bayan Halartar Wani Taro Kan Zaben Shugaban Kasa
Shugabar karamar hukumar Calabar ta Kudu a jihar Cross River, Misis Esther Bassey ta rasu.
Majiyoyi sun shaida wa Daily Trust cewa Bassey ta rasu ne bayan halartar wani taro kan yadda za a kammala dabarun zaben na ranar Asabar.
Da yake tsokaci game da ci gaban, daya daga cikin hadiman marigayiyar ya ce marigayiyar shugabar wanda aka fi sani da Sarauniyar Kudu ta kasance cikin nutsuwa da jin dadi a daren jiya.
“Ta halarci tarurruka da dama domin shiryawa zaben shugaban kasa na gobe. Ta yi wasu tarurruka jiya kusa da dare.
“Ba ta nuna alamun gajiya ko rashin lafiya ba lokacin da ta ta tashi daga taron daga baya da maraice”, in ji daya daga cikin mataimakan.
Rahotanni sun ce tsohuwar shugabar karamar Hukumar ta rasu ne a cikin barcinta da misalin karfe 4 na safe a Calabar.
