News
An kama wani dan kasuwa da Miyagun Kwayoyi mai nauyin kilogiram 9.40 a filin jirgin saman Legas
Jami’an hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa sun cafke wani dan kasuwa mai suna Kingsley Celestino mai shekaru 49 a filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke Ikeja jihar Legas dauke da kilo 9.40 na tabar heroin da ya boye a cikin jakunkuna biyu na tafiya.
An kama Kingsley, dan asalin karamar hukumar Nnewi ta Kudu a jihar Anambra, a Terminal 2 na filin jirgin sama a kan hanyarsa ta zuwa Indiya ranar Asabar.
Messi na shirin buga Argentina wasa a karon farko tun bayan lashe kofin duniya a Qatar a 2022.
Hukumar ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da ta fitar ta shafin Facebook a ranar Lahadi.
“Rundunar hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA, ta kama wani dan kasuwa mai suna Kingsley Celestino a filin jirgin sama na Murtala Muhammed dake Ikeja Legas sama da kilogiram 9.40 na tabar heroin da aka boye a cikin jakunkuna biyu.
“An kama Kingsley, wani fasinja aji a jirgin Qatar Airline a Terminal 2 na MMIA a ranar Asabar 4 ga Maris akan hanyarsa ta zuwa Indiya. Duk da cewa dan asalin karamar hukumar Nnewi ta Kudu ne a jihar Anambra, dan shekaru 49 yana tafiya ne da fasfo din kasar Guinea.
“Bincike na farko ya nuna cewa wanda ake zargin yana yawan tafiya Indiya akan tikitin kasuwanci. Ya yi ikirarin cewa yana huldar kasuwanci tsakanin Najeriya da Indiya. An kara tabbatar da cewa ya samu fasfo din kasar Guinea a Guinea Bissau, inda ya ce mahaifiyarsa ta fito.”
