News
An yi artabu tsakanin masu zanga-zanga da jami’an ‘yan sanda a Girka.
‘Yan sandan kwantar da tarzoma sun yi artabu da dubban masu zanga-zanga da suka yi dandazo a harabar majalisar dokoki ta birnin Athenses a wannan Lahadi, kwanaki bayan mummunan hadarin jirgin kasa da ya halaka mutane 57.
Masu boren sun yi ta kone-konen kwandunan shara da jefa wa ‘yan sanda wasu abubuwan fashewa, a yayin da su kuwa jami’an tsaron, suka yi ta harba gurnetin hayaki mai sa kwalla don tarwatsa zanga-zangar.
An kama wani dan kasuwa da Miyagun Kwayoyi mai nauyin kilogiram 9.40 a filin jirgin saman Legas
Wannan lamarin na zuwa ne duk da binicken da hukumomin kasar suka fara kan hadarin na wannan makon, inda yanzu hakan wani alkali a birnin Larissa ya bukaci a gurfanar da shugaban babbar tashar jiragen kasa na kasar bisa tuhumarsa da yin sakacin da ya kai ga mutuwar al’umma.
Bayan jagoran akwai yiwuwar a gurfanar da shugabannin kafanin sufurin jiragen kasar ta Girka na “Hellenic Train” a cewar wasu majiyoyin shari’ar kasar.
