Connect with us

News

Miji Ya Hallaka Matarsa A Kan Ruwan Sha

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

‘Yansanda a Jihar Legas sun cafke wani magidanci mai shekara 49, mai suna Lawrence Itape, da ke zaune a yankin Ajah bisa zargin kashe matarasa ta hanyar daba mata wuka.

 

Advertisement

Kakakin rundunar ‘yansandan jihar, wanda ya tabbatar da hakan, ya ce, Lawrence, ya kashe mai dakinsan ne, saboda cacar bakin da ta kaure a tsakaninsu a kan karancin ruwan sha a sashen rukunin gidajen da suke haya.

Davido zai yi wasa a bikin rufe Gasar cin Kofin Duniya a Qatar

 

Advertisement

Leadship hausa ta rawaito cewa Benjamin ya ce, bayan an kawo rahoton aukuwar lamarin, DPO mai kula da caji ofis na yankin Langbasa, Stephen Abolarin, ya tura Jami’ansa zuwa inda lamarin ya auku, inda suka kamo Lawrence tare da kwato wukar da ya yi amfani da ita wajen aikata ta’asar.

 

Advertisement

A cewar Benjamin, an tura maganar da kuma Lawrence zuwa ga sashen gudanar da bincike na SCIID da ke a yankin Panti, Yaba a jihar don a gudanar da dogon bincike.

 

Advertisement

Ya ce, an kai gawar matar zuwa dakin ajiye gawarwaki na babban asibitin Mainland da ke a Yaba don yin gwaji.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending