Sports
Badakalar rashawa ta rage armashin wasan El Clasico
Tuhumar da ake yi wa Barcelona akan bai wa alkalin wasa cin hanci ta rage armashin wasa mafi girma a duniyar kwallon kafa da aka fi sani da El Clasico, wanda ake kece-raini a tsakanin kungiyar ta Barcelona da babbar abokiyar hamayyarta Real Madrid.
A ranar Lahadin nan ne dai za a yi karon batta tsakanin kungiyoyin da ke gasar La Liga ta Spain.
A makon da ya gabata, lauyoyin gwamnati a Spain suka shigar da kara gaban kotu, inda suke tuhumar Barcelona da biyan kudin da yawansu ya kai euro miliyan 7 ga kamfanin tsohon mataimakin shugaban kwamitin alkalan wasa na Spain Jose Maria Enriques Negreira, a tsakanin shekarar 2001 zuwa 2018.
Sai dai kungiyar ta kare kanta da cewar, ta biya miliyoyin euron ne domin ba ta rahotannin kwararru da kuma shawara akan alkalancin wasa, amma ba domin samun alfarma ta musamman ba dangane da hukunce-hukuncen da alkalan wasa ke yankewa ba.
TALLA
Karar da lauyoyin gwamnatin Spain suka shigar dai ta shafi tsaffin shugabbannin Barcelona ne da suka hada da Sandro Rosell da kuma Josep Maria Bartomeu, sai kuma Jose Maria tsohon babban jami’in kwamitin alkalan wasa.
Duk da cewar Barcelona na da dama mafi rinjaye ta lashe kofin gasar La Liga na bana da tazarar akalla maki 12 idan ta lallasa Real Madrid a karawar da za su yi, badakalar rashawar da ake zargin Barcelona na da hannu dumu dumu a ciki, na cigaba da daukar hankalin masu ruwa da tsaki akan kwallon kafa.
Tuni dai tawagar ‘yan wasan Barcelona ta fara fuskantar tsangwama kan zargin da take fuskanta na bai wa alkalan wasa rashawa, inda a wasan da suka buga a ranar Lahadin da ta gabata, wasu magoya bayan Athletic Bilboa suka rika jefa takardun kudade a cikin fili dauke da tambarin Barcelonan da kuma rubutun ‘Mafiya’ a turance, abinda ke nufin ‘Miyagu’
