News
Yan Bindiga Sun Sace Wani Fitaccen Dan Kasuwa a kano
Wasu yan bindiga sun yi garkuwa da wani attajiri a kauyen Gangarbi da ke karamar hukumar Rogo a Jihar Kano.
Yan bindigar sun kuma harbi mutum biyu da suka yi yunkurin hana su tafiya da dan kasuwar inda daya ya mutu nan take Rundunar yan sandan jihar ta tabbatar da faruwar lamarin sai dai ba ta bada cikakkiyar masaniyar lamarin kamar yanda jaridar punch ta rawaito
Ƴan sanda na neman amaryar da ta yi harbi da bindiga lokacin bikinta
Wani shaidar gani da ido kuma dan uwan wanda aka sace da ya nemi a sakaya sunan shi, ya ce yan bindigar sun mamaye yankin tare da harbe-harbe don tsorata mazauna yankin.
Ya ce ‘yan bindigar sun kai farmaki gidan dan kasuwar ne da misalin karfe 12 na safe, inda suka isa wurin, sai suka fara harbe-harbe a iska, lamarin da ya dauki hankulan makwabtan dan kasuwar.
“Lokacin da mutanen yankin suka yi yunkurin hana ‘yan bindigar tafiya da wanda abin ya shafa, sun harbe mutum biyu, lamarin da ya kai ga mutuwar daya nan take, wani kuma ya samu rauni kuma a halin yanzu yana samun kulawa a asibiti,” inji ganau din.
An tattaro cewa kauyen Gangarbi da kauyukan da ke makwabtaka da shi, kamar Bari da Gwangwan sun fuskanci hare-haren ‘yan bindiga a kwanakin baya.
Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kano, SP Abdullahi Haruna, ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce yana jiran jami’in ‘yan sanda na yankin ya ba shi cikakken bayani kan lamarin.
Sai dai ya tabbatar da cewa zai koma ga wakilinmu da zarar ya samu cikakken bayani.
