Connect with us

Sports

Southampton ta jikawa Arsenal aiki a Emirates

Published

on

 

 

Advertisement

Da kyar Arsenal, da ke saman teburin Firimiya, ta iya rike Southampton a wasan da suka yi a ranar Juma’a da daddare inda suka tashi da ci 3-3.

 

Advertisement

Tun da aka murza leda Southampton ta nuna tana son ta doke Arsenal ganin yadda ta zura kwallo uku a ragar Arsenal yayin ta take da ci daya.

 

Advertisement

Har zuwa minti 86 Southampton tana da ci uku ne yayin da Arsenal ke da ci daya.

Dalibai Sun Daina Zuwa Makaranta Sun Koma Harkar Yahoo.

Sai dai cikin minti huɗu Arsenal ta farke kwallaye biyu.

Advertisement

 

Odegaard ya zura wa Arsenal kwallo a minti 88, yayin da Saka ya zura mata ɗaya kwallon a minti 90.

Advertisement

 

Sakamakon wasan na nufin Arsenal tana gaban Manchester City, wadda ke neman kwace saman teburin Firimiya daga hannunta, da maki biyar kacal bayan ta sake zubar da maki biyu .

Advertisement

 

Tun da City tana da dakon wasa biyu, za ta iya shan gaban Arsenal idan ta iya nasara a wasannin da suka rage mata.

Advertisement

 

Sai dai kuma kocin Arsenal Mikel Arteta ya sha alwashin doke City a gida a karawar da za su yi a Etihad ranar Laraba.

Advertisement

 

Tun shekarar 2015 dai Man City ba ta sha kaye a gida a hannun Arsenal ba.

Advertisement

 

Amma a jawabin da ya yi bayan sun sha da kyar a hannun Southampton, Arteta ya ce ” wannan wani mawuyacin lokaci ne. Lokaci ne da ya kamata mu hada kanmu har zuwa karshe.

Advertisement

 

Muna da abubuwa da dama da muke bukatar yi a wannan kakar. Gasar ba ta kare ba. Kawo yanzu muna gaba da maki biyar. “.

Advertisement

 

Bayan Arsenal ta barar da maki shida a wasanni ukun da ta yi kwanan nan, babu tabbacin cewa za ta iya nasara a wasanni shidan da suka rage mata a gasar Firimiyar bana.

Advertisement

 

Sai dai Arteta na ganin yaransa, wadanda suka fi na ko wacce kungiya kuruciya a gasar Firimiya kakar bana, za su yi iya kokarinsu a gidan City.

Advertisement

 

”Dole mu je mu yi nasara a can (Etihad),” in ji Arteta.

Advertisement

 

Ranar Laraba za a sani ko Arsenal za ta iya cika wannan burin na kocinta.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending