Connect with us

News

INDARANKA :Matashi ya kashe mahaifiyarsa sannan ya kwana 2 yana lalata da gawarta

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

Wani matashi ya bayyana yadda ya kashe mahaifiyarsa sannan ya kwana biyu da gawarta a daƙi yana zina da gawar kafin daga bisani ya yanƙe farjinta ya kai wa boka don yayi masa tsafi dashi na kuɗi.

Matashin ɗan shekara 18 mai suna Kingsley Akpobome Emobor, wanda ɗan asalin garin Oghara dake jihar Delta ne ya aikata wannan ta’asar ce a gidan su dake garin Ikpoba-Okha Ologbo dake yankin ƙaramar hukumar Ikpoba-Okha a jihar EDO.

Wasu Yan bindiga sun sace manoma a jihar Neja

Jaridar gaskiya tafi kabo ta ruwaito cewa asirin matashin ya tonu ne bayan da wani kawunsa yaga kwana biyu bai ga mahaifiyar matashin ba, saboda haka ya yanke shawarar ziyartar gidansu don ya je yaji ko lafiya, bayan isar sa gidan ke da wuya sai yaga gawarta kwance cikin jini har ta fara ruɓewa.

Bayan ganin wannan lamari ne sai ya fantsama cikin gari ya nemi taimakon jama’a domin su zo su ga halin da ya tsinci ‘yar uwarta shi a ciki, daga nan ne kuma aka shiga neman ɗan ta don jin yadda aka yi aka haihu a ragaya.

Bayanai sun ce bayan kama Kingsley Akpobome Emobor, an tambaye shi kan abin da ya faru, ya shaida cewa, shi da kansa ya kashe mahaifiyartasa, sannan yayi zina da gawarta har na tsawon kwana biyu daga bisani ya yanƙe farjinta ya kai wa boka domin ya yi masa kuɗi.

Advertisement

Matashin sarkin katoɓara ya shaidawa yan sanda cewa, boka ne ya umarce shi da ya kashe mahaifiyarsa, sannan yayi kwana biyu yana lalata da gawarta, in ya kammala sai ya yanƙe farjinta ya kai masa, zai yi arziki da sai sunansa ya karaɗe ko ina a Nigeria.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending