Connect with us

Sports

Barcelona Ta Lashe La Liga Karon Farko Bayan Shekaru Hudu

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

Barcelona ta lashe gasar La Liga a karon farko cikin shekaru hudu, bayan samun nasarar lallasa Espanyol da ci 4-2 a wasan da suka fafata a ranar Lahadi.

Advertisement

Robert Lewandowski ne ya ci wa Barcelona kwallaye biyu sai kuma na farko tun bayan zuwansu Barca da Alejandro Balde da Jules Kounde suka jefa wa kungiyar.

Wasu ma’aikatan Banki sun kashe matar wani Magidanci dayaci Bashin Banki kuma ya gaza biya.

A yanzu Barcelona ta bai wa Real Madrid tazarar maki 14 da ke biye da ita a mataki na biyu yayin da ya rage wasanni hudu a karkare La Liga ta bana.

Advertisement

Barca ce kungiyar da babu kamarta a fagen tamaula a Sifaniya a bana, inda ta rika jan ragama a saman teburin La Liga tun daga wasan mako na 13.

Barcelona ta lashe La Liga jimilla 27 a tarihi, kuma wannan ita ce ta kakar wasa ta farko da tsohon dan wasan kungiyar, Xavi Hernandez ya jagorance ta a matsayin koci.

Advertisement

Sai dai duk da wannan bajinta da Barcelona ta yi a iya La Liga, ta gaza kai bantenta a nahiyar Turai, inda aka tankado keyarta tun daga zagayen rukuni a Gasar Zakarun Turai, sannan kuma bayan ta koma Gasar Europa, a can ma Manchester United ta yi wancakali da ita.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending