Connect with us

News

Buhari Ya Zama Tsohon Shugaban Najeriya

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Advertisement

 

Bayan kammala wa’adin shekara 8 Muhammadu Buhari ya zama tsohon shugaban Najeriya

Advertisement

Bayan mika mulki ga Tinubu Buhari da ‘yan tawagarsa sun fice daga filin taron rantsuwa cikin ayarin motoci.

Tuni aka  tsaurara matakan tsaro a garin Daura, mahaifar shugaban kasa Muhammadu Buhari mai barin gado, gabanin komawarsa bayan rantsar da zababben shugaban kasa a yau.

Advertisement

Buhari Ya Kaddamar Da Kwalejin Sojojin Ruwa Da Sashen Tashi Da Saukar Jiragen Sama Na Kasashen Ketare A Kano

Buhari zai koma Daura bayan mika mulki ga  sabon shugaban kasa a Abuja.

Za a kai shi Katsina daga Abuja daga bisani kuma a kai shi Daura a wannan rana.

Advertisement

A fadar sarkin Daura, an sanya alluna a bakin kofar da ke dauke da sakonnin da ke cewa shugaban ya yi nasarar kammala wa’adinsa kuma ya yi wa kasa hidima.

Haka kuma garin yana karbar baki saboda babu ragowar daki a otal din Daura Motel wanda ya kasance daya tilo da ke Daura.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending