Connect with us

News

Yan sanda sun kuɓutar da yara tara a Zamfara

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

 

Advertisement

Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya ta kubutar da wasu kannana yara tara da ‘yan bindiga suka sace.

A cikin wata sanarwa da Rundunar ‘yan sandan jihar ta fitar mai ɗauke da sa hannun kakakin rundunar jihar ASP Yazid Abubakar, ya ce a ranar 3 ga watan Yuni ne rundunar ta samu bayanai daga dagacin ƙauyen Gora Namaye cewa ‘yan bindiga sun sace wasu yara maza da mata waɗanda suka tafi neman itace a jeji.

Advertisement

Dan Takarar Gwamna A Kogi Ya Dauki Malamin Firamare A Matsayin Mataimaki

Sanarwar ta ce bayan samun labarin ne ‘yan sanda tare da hadin gwiwwa jami’an tsaro suka ƙaddamar da bincike domin ceto yaran, lamarin da ya sa suka samu nasarar ceto yaran tara, tare da mayar da su hannun iyayensu.

Rundunar ta ce tana ci gaba da gudanar da bincike domin kamo maharan tare da gurfanar da su a gaban kotu.

Advertisement

A ranar Asabar ne ‘yan bindigar suka kai hari tare da sace yaran a ƙauyen Gora da ke cikin yankin ƙaramar hukumar Maradun a jihar zamfara.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending