News
wasu matasa sun kewaye tsohon ginin kamfanin jaridar Triumph inda aka gina rukunin shaguna na zamani suna kokarin kwashe kayayyakin dake ciki.
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Rahotanni daga karamar hukumar Fagge da ke jihar Kano na nuni da cewa wasu matasa sun kewaye tsohon ginin kamfanin jaridar Triumph inda aka gina rukunin shaguna na zamani masu hawa uku suna kokarin kwashe kayayyakin dake ciki.
Ganau sun tabbatarwa Arewa Radiyo cewa masu kwangilar aikin sun shiga ciki da mota domin kwashe wasu kayayyaki bayan wasika da ake zargin an rubuta kan rushe ginin.
Duk da cewa an girke Jami’an tsaro a kofar shiga, matasan sun balle kofar bayan ginin tare da fara cire kifofi da tagogi.
Advertisements
