Connect with us

News

An fara cire tsammaninn ceto attajiran da suka nutse a teku

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

 

Advertisement

An fara cire tsammani kan fatan gano hamshakan attajiran nan masu yawon bude ido da suka bace a karkashin tekun Atlantic tun a ranar Lahadin da ta gabata.
Tuni dai kwararru suka yi gargadi cewar ragowar Iskar Oxygen din da ke cikin karamin jirgin ruwan mai nutsawa karkashin teku ta kare da misalin karfe 10 na safiyar yau Alhamis.

Shin Da Gaske An Bude Bodar Legas Don Shigo Da Motoci?

Jirgin karkashin ruwan mai suna Titan da ke da tsawon kusan mita 7, ya fara nutsawa zuwa karkashin teku ne da zummar isa ga ragowar tarikicen katafaren jirgin ruwan nan na Titanic da yayi hatsari a shekarar 1912 ne da misalin karfe tsakwas na safiyar ranar Lahadin da ta gabata.

Advertisement

Sai dai kasa da sa’o’i biyu, bayan fara nutsun musayar bayanai da jirgin ta katse.

A halin da ake ciki, daruruwan jami’an ceto sun fadada laluben da suke yi zuwa fadin murabba’in kimanin kilomita dubu 26 akan teku, tare da nisan kilomita 4 zuwa karkashin ruwan.

Advertisement

Wannan aikin ceto da jami’an agaji na kasa da kasa suka bai wa muhimmanci na zuwa ne a daidai lokacin da wasu ke ganin hukumomin na kasa da kasa ba su damu da rayukan dubban ‘yan ci ranin da ke salwanta a teku ba, duk da cewar dokokin majalisar dinkin duniya sun fayyace cewar tilas a kai daukin gaggawa tare da ceto duk wanda ya shiga hatsari a teku, tare da haramtawa gwamnotocin kasashe daukar matakin hana jiragensu na ruwa ko jami’ansu shiga ayyukan ceto.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending