News
Hukumomin EFCC Da DSS Sun Kusa Kammala Binciken Sunayen Ministocin Shugaban Najeriya Tinubu
Alamu na nuna cewa hukumar EFCC da DSS, da wasu jami’an tsaro na gab da kammala bincikensu na wajibi akan jerin sunayen ministocin shugaba Bola Tinubu.
Jaridar Punch ta rawaito cewa hukumar DSS da mambobin kwamitin shugaban kasa na gudanar da bincike na karshe a kan mutanen da aka sanya sunayensu a matsayin ministoci.
Kungiyoyin Yaki Da Rashawa Sun Bukaci A Sanya Idanu Akan Tsohon Gwamnan Kano Ganduje
Majiyoyin fadar shugaban kasa da dama sun tabbatarwa da jaridar Punch cewa nan ba da jimawa ba za a fitar da jerin sunayen kafin wa’adin watanni biyu kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanada.
Tsammanin ‘yan majalisar dokoki da sauran ‘yan Najeriya ya karu na Jiran ganin abunda ke cikin jerin sunayen ministocin, yayinda da shugaba Bola Tinubu ya cika kwanaki 40 a kan karagar mulki.
-
News7 days agoShekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano
-
News3 days agoKotu Ta Daure Wani Limamin Masallacin Juma’a Wata 1 Kan Tura Bidiyon Tsaraici Ga Matar Aure A Kano
-
News5 days agoƘalubalen Da Masu Ƙananan Sana’o’i Ke Fuskanta Saboda Ƙarancin Wutar Lantarki A Kano
