Connect with us

News

Hukumar tsaro ta farin kaya DSS ta musanta cewa an kama Sanata Abdulaziz Yari ne saboda ya ki amsa kiran wayar shugaban kasa Bola Tinubu.

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

 

Advertisement

Hukumar tsaro ta farin kaya DSS ta musanta cewa an kama Sanata Abdulaziz Yari ne saboda ya ki amsa kiran wayar shugaban kasa Bola Tinubu.

Kakakin hukumar ta DSS, Dakta Peter Afunanya, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar kuma ya wallafa a shafin Twitter a ranar Lahadi, inda ya bayyana ikirarin a matsayin abin dariya da kuma rashin dacewa.

Advertisement

Hukumomin EFCC Da DSS Sun Kusa Kammala Binciken Sunayen Ministocin Shugaban Najeriya Tinubu

Sanarwar ta tabbatar da gayyatar Yari, inda ta ce Sanatan ya san dalilin gayyatarsa.

Har ila yau, sanarwar ta musanta zargin cewa hukumar na tuhumar alkalan kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa.

Advertisement

Sanarwar ta kuma musanta rahotannin da ke cewa hukumar ta DSS ta mamaye ofisoshin ICPC da hukumar ‘Da’ar ma’aikata tare da kwashe wasu takardu daga hannunsu.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending