Connect with us

News

Dole Gwamnatoci Su Kare Masu Fallasa Rashawa A Afirka – Amnesty

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

 

Kungiyar kare hakkin bil’adam ta Amnesty International, ta ce dole ne kasashe yammaci da tsakiyar Afirka su daina cin zarafin masu bankaɗo ayyukan rashawa, a maimakon hakan sai a dauki matakan kare su.

Jiya ne aka cika shekara 20 da cimma yarjejeniya kasashen Afirka ta kiyayewa da kuma yaki da rashawa.

NNPCL ya kama jirgin ruwa dauke da danyen mai na sata da za a kai Kamaru

Babbar sakatariya a kungiyar ta Amnesty, Agnes Callamard, ta ce “Irin halin da masu fallasa rashawa ke shiga a kasashen yammaci da tsakiyar Afirka abin babu dadi, wadannan mutanen fa mutane ne da ke taka muhimmiyar rawa da sadaukarwa wajen yaki da cin hanci da rashawa, to amma sai kaga daga karshe su ake kai wa hari ko wulakanta su saboda kawai sun bayyana gaskiya.”

Ta ci gaba da cewa,” Dole ne gwamnatoci su tashi tsaye wajen kare hakkin dan’adam da girmama masu kwarmata irin waɗannan bayanai da ma biya musu dukkan bukatunsu saboda rawar da suke takawa wajen bayyana marassa gaskiya.”

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending