Connect with us

News

Mutum uku sun mutu a sakamakon hadarin jirgi mai saukar ungulu

Published

on

Hatsarin jirgi

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

 

Advertisement

Wani hadarin jirgi mai saukar Angulu a arewa maso gabashin Congo yayi sanadin mutuwar mutane uku, a cewar mahukuntan yankin da lamarin ya faru.
Jirgin mai saukar Angulu, mallakin wani kamfanin hakar ma’adanai ya fadi ne cikin daren jiya lokacin a yake kokarin isa wani wajen aikin hakar ma’adanai da ke yankin Lualaba.

Cikin mutane ukun da suka mutu, akwai shugaban kamfanin hakar ma’adanan, da kuma shugaban wani kamfanin hakar ma’adanai mai suna G4S da kuma matukin jirgin dan asalin kasar Faransa.

Advertisement

SUDAN:Hari kan kasuwa a birnin Khartoum ya hallaka mutum 34

Har yanzu dai babu wani cikakken bayani kan dalilin faduwar jirgin, sai dai kawo yanzu tuni aka kai gawarwakin dakin adana gawa na asibitin garin Lubumbashi da ke dab da inda hadarin ya auku.

Kasar Congo na cikin kasashen Africa da ke kan gaba wajen albarkar ma’adanin Lithium da ake amfani da shi, wajen hada baturan na’urorin lantarki, sai kuma albarkar Copper da aka samo a baya-bayan nan.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending