Connect with us

News

KAROTA ta sami nasarar cafke wasu matasa biyar masu sojojan gona da hukumar

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

Hukumar kula da Zirga-zirgar Ababen Hawa ta jiha KAROTA ta sami nasarar cafke wasu matasa biyar masu sojojan gona da hukumar

Shugaban Hukumar KAROTA Engr. Faisal Mahmud Kabir ne ya bayyana haka a yau ta cikin wata sanarwa da Kakakin Hukumar ta KAROTA Nabilusi Abubakar Kofar Nai’sa ya sanya wa hannu

Dalilan Da Ya Sa Shugaban Jamiyyar APC Na Kasa Ya Yi Murabus

Ya bayyana cewa an jima ana kawo ƙorafi hukumar cewa jami’anta na matsawa al’umma da karɓe-karɓen kuɗi

Bayan zurfafa bincike a wannan rana an sami nasarar cafke mutum biyar daga cikin wadanda ake zargin

Advertisement

Sanarwar ta bayyana cewa Shugaban Hukumar ya ce za a dauki matakin gurfanar da su a gaban Yansanda domin zurfafa bincike tare da ɗaukar matakin da ya dace.

Shugaban ya roƙi al’umma da su ci gaba da bawa Hukumar KAROTA haɗin kan da ya dace domin gudanar da ayyukanta bisa tsarin doka da oda.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending