News
SUDAN:Ana ci gaba da luguden wuta a wasu yankuna na kasar Sudan
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADEEN
A kasar Sudan ana ci gaba da luguden wuta a birnin Khartoum da ma yankin yammacin Dafur a cewar shaidun gani da ido, duk da yunkurin kawo karsehn rikicin da kashen duniya ke yi.
Wani mumunan hari da aka kai ta sama a garin Ombada mai yar tazara da birnin Khartoum, ya yi sanadiyar rayukan mutane 5 yayin da wasu 17 suka jikkata.
Masu aikin ceto na ci gaba da neman mutane da suka makale a baraguzen gine-gine, lamarin da ya sa ake ganin adadin wadanda suka mutu ka iya karuwa.
Ya zuwa yanzu, sama da mutum dubu uku ne rikicin na Sudan mai tushe da batun shugabanci suka rasa rayukansu, a cewar wata kungiya mai tattara bayanan yaki, amma kuma wasu na ganin adadin ya zarta haka.
A jiya Asabar ne aka koma teburin tattaunawa a tsakanin sojojin gwamnati da na dakarun RSF a birnin Jeddah na kasar Saudiyya. Zaman da kawo yanzu babu rahoto a kan yadda ya kaya, a baya an yi irinsa ba tare da cimma matsayar kawo karshen yakin ba.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News6 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News3 days ago
Gwamna Abba Ya Ayyana Murtala Sule Garo A Matsayin Wanda Zai Yi Masa Takarar Mataimakin Gwamna A Zaɓen 2027
