News
An Kama Dillalan Kwaya 617 a Kano.—NDLEA
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya (NDLEA) ta yi nasarar kame wasu bata garin da ake zargin suna harkallar miyagun kwayoyi a jihar Kano.
Wannan na fitowa ne daga bakin kwamandan hukumar na jihar, Abubakar Idris a lokacin da yake zantawa da gidan talabijin na Channels Tv, inda ya bayyana cewa, akalla mutane 619 ne aka kama da miyagun kwayoyin a yankin Sabon Gari.
Yan Bindiga A Zamfara Sun Yi Barazanar Auren ‘Yan Mata 4 Da Ke Hannunsu
A cewar sa wadanda aka kama din ba kawai masu shan kwaya bane, an kama wadanda ke dillacin miyagun kwayoyin ne tare da kwace wasu kayayyaki.
Ya kuma bayyana cewa, kayayyakin da aka kwato sun fi karfin a ce na mashaya kwayoyin ne, sun fi kama da na wadanda ke dillacin miyagun kwayoyi.
Ya kara da cewa, wadanda aka kaman tuni aka bincike su kana aka mika su ga kotu domin tabbatar da adalci da hukunci a kansu.
“Da yardar Allah mun yi nasarar gurfanar da wadanda ake zargi 619.
Idan ina magana a kan wadanda ake zargi, ina nufin wadanda aka kama, aka bincika kana aka gurfanar, ba wai kawai mashaya ba.
“Ba wai irin wadanda ake kama wa da daya biyu na miyagun kwayoyi ba, ina magana ne kan dillalai masu siyar da mai yawa wadanda su ne muka gurfanar da 619.”
Bincike ya bayyana cewa, akalla mutane sama da miliyan 2 ne ke kwankwadar kayan bugarwa a jihar Kano, wanda ke wakiltar sama da kaso 16% na mazauna jihar.
Hukumar NDLEA na ci gaba da kokarinta wajen kamawa da gurfanar da masu shaye-shaye da dillalan miyagun kwayoyi a jihar.
A gefe guda, ana ci gaba da ladabtarwa da daura tubabbun ‘yan shaye-shaye a turbar daina shan kwaya kwata-kwata a gidan gyaran hali.
