Connect with us

News

Majalisar Dinkin Duniya ta dakatar da ayyukan jinkai a Nijar bayan juyin mulki

Published

on

sojojin Jamhuriyar Nijar sunyi juyin mulkin.

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN.

 

Advertisement

Ofishin Ayyukan Jinkai na Majalisar Dinkin Duniya, OCHA, ya dakatar da dukkan ayyukansa a Jamhuriyar Nijar bayan juyin mulkin da sojojin kasar suka yi.

A wata sanarwa da Ofishin Ayyukan Jinkai na Majalisar Dinkin Duniyaya fitar da maraicen ranar Alhamis, ya ce “Sakamakon abubuwan da ke faruwa a Nijar, mun dakatar da ayyukan jinkai da muke yi a can, inda da ma kasar ke fuskantar yanayin jinkai mai sarkakiya da ke da alaka da karuwar tashin hankali da kalubalen zamantakewa da kuma sauyin yanayi.”

Advertisement

Rundunar Yan sandan za ta gurfanar da Shahararren dan wasan barkwanci, a gaban kuliya. 

Fadar shugaban kasar Nijar ta tabbatar da cewa sojojin kasar wadanda suka toshe hanyoyin shiga fadar tun a ranar Laraba sun hambarar da Shugaba Mohamed Bazoum.

A yayin da yake ayyana goyon bayansa ga dakarun da suka kaddamar da juyin mulkin, shugaban rundunar sojin kasar ya ce matakin ya zama dole ne don “a hana mummunan fito-na -ito tsakanin rundunoni daban-daban.”
Yawan mutanen da ke bukatar agaji ya karu daga miliyan 1.9 a 2017 zuwa miliyan 4,3 a 2023 a Nijar, a cewar Ofishin Ayyukan Jinkai na Majalisar Dinkin Duniya

Advertisement

Fiye da mutum 370,000 ne suka rabu da muhallansu da suka warwatsu a cikin kasar don neman mafaka, baya ga ‘yan gudun hijira 250,000 da da ma suke neman mafaka a kasar – wadanda suka je daga kasashe irin su Nijeriya da Mali da kuma Burkina Faso.

Kazalika ana sa ran yawan masu tsananin bukatar abinci zai karu daga miliyan 2.5 zuwa miliyan uku a lokacin damina, daga tsakanin watan Yuni zuwa Agusta, a cewar hukumar ta majalisar dinkin duniya.

Advertisement

A yanzu haka majalisar dinkin duniya ta ware dala miliyan 584 don aiwatar da ayyukan agaji a kasar.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending