News
Shirin kungiyar ECOWAS na tura sojoji Jamhuriyar Nijar yana tangal-tangal
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN.
A yau ne wa’adin da kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka, ECOWAS, ta bai wa sojojin da suka kifar da gwamnati a Jamhuriyar Nijar da su mayar da Mohamed Bazoum kan mulki yake cika.
Ranar Lahadin da ta gabata ne kungiyar ta sanya wa Nijar takunkumai ciki har da rufe iyakokinta da kasar a yunkurinta na matsa lamba ga sojojin su mika mulki ga gwamnatin farar-hula da suka tumbuke.
Gwamnonin PDP sun gargadi Tinubu da ya rungumi diflomasiyya, da tattaunawa
A taron da ECOWAS ta yi na makon jiya, ta sha alwashin yin amfani da karfin soji a matsayin mataki na karshe don mayar da gwamnatin dimokuradiyya a kasar.
Sai dai da alama sojojin ba su yi ko gezau ba. Hasalima sun sha alwashin mayar da martani mai karfi kuma cikin hanzari kan duk wata barazana da za a yi musu daga kasashen waje.
Wa’adin da ECOWAS ta bai wa sojojin Nijar na cika ne a yayin da ake kara samun adawa daga bangarori daban-daban na tura sojoji kasar ta Nijar.
Ranar Asabar da maraice, Aljeriya ta zama kasa ta baya-bayan nan da take adawa da yin amfani da karfin soji kan sojin da suka yi juyin mulki a Yamai.
“Amfani da karfin soji zai haifar da gagarumin rikici a duka yankin Sahel don haka Aljeriya ba za ta yi amfani da karfi kan makwabtanta ba,” in ji wata sanarwar da ta ambato shugaban kasar Abdelmadjid Tebboune yana fitarwa a gidan talbijin na Ennahar, a cewar kamfanin dillancin labarai na Reuters.
