Connect with us

News

Wata Gawa ta yi layar zana ana shirin jana’izarta

Published

on

Gawa

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN.

Bacewar gawar wata dattijuwa mai shekara 63 a yayin da ake shirin gudanar da jana’izarta a ranar Asabar ya haifar da rudani a Jihar Ondo.

Advertisement

Gawar Misis Olajumoke Julianah Ogunsuyi ta yi batan dabo ne a dakin ajiyar gawan da ke unguwar Osii da ke garin Akure inda iyalanta, inda iyalanta suka kai gawar da nufin yi mata janaz’iza ranar Asabar.

Shirin kungiyar ECOWAS na tura sojoji Jamhuriyar Nijar yana tangal-tangal

Amma da ranar Juma’a suka je mutuwaren da ke Asibitin koyarwa na jami’ar aikin likita (UNIMED) domin daukar gawar, sai aka nemi gawar sama da kasa aka rasa.

Advertisement

Wata majiya mai kusanci da iyalan ta ce, “bayan mun shafe awowi muna jiran masu kula da mutuware su fito da gawar Misis Ogunsuyi, abin mamaki ba a ga gawar ba.”

Wata majiyar ’yan sanda ta ce ’yan sanda sun gayyaci jami’an asibitin da masu kula da mutuwaren domin amsa tambayoyi.

Advertisement

Ya ce daga baya an gano an yi musayar gawar tata ce da wata wadda za a binne a garin Oba a bisa kuskure.

FRI ta rawaito cewa ta yi kokarin samun karin bayani daga kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Ondo, Funmilayo Odunlami-Omisanya, bai yi nasara ba.

Advertisement

Wakilin namu ya tura mata rubutaccen sako amma bai samu amsar sakon ba.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending