Connect with us

News

Rikicin Siyasar Jihar Ondo Na Kara Daukar Sabon Salo

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Advertisement

Magoya bayan mataimakin gwamnan jihar Ondo, Hon Lucky Aiyedatiwa da na gwamnan jihar, Rotimi Akeredolu, na shirin gudanar da wata gagarumar zanga-zanga a Akure, babban birnin jihar Ondo, a cikin makon nan.

Magoya bayan mataimakin gwamnan sun sanar da shirye-shiryen zanga-zangar a shafukan sada zumunta daban-daban a karshen mako, kamar yadda magoya bayan Akeredolu suma suka sha alwashin gudanar da zanga-zangar adawa.

Advertisement

Idan Za’a Sake Zaben Zamfara Sau 100 Sai Na Lashe — Gwamna Dauda

Dan majalisar wakilai Kokade Akinjo ne ke jagorantar zanga-zangar adawa da Akeredolu.

Sai dai , wata kungiya a jihar am ta yi kira ga magoya bayan gwamnan da mataimakinsa da su maida takubansu cikin kube domin tabbatar da zaman lafiya a jihar.

Advertisement

A wani labarin kuma Idan Za’a Sake Zaben Zamfara Sau 100 Sai Na Lashe — Gwamna Dauda

Sojojin Isra’ila sun ce sun yi wa birnin Jabalia da ke arewacin Gaza ƙawanya, inda ta ce dakarunta sun shirya ɗaukar mataki na gaba.

Advertisement

Jabalia na a arewacin birnin Gaza, wanda ya fuskanci kazamin faɗace-faɗace tun soma yaƙin.

A wata sanarwa sa’o’i kaɗan da suka wuce, dakarun tsaron Isra’ila sun ce sun kai hare-hare kan shingayen Hamas 250 a ranar Litinin ta hanyar amfani da jiragen yaƙi da ake sarrafasu.

Advertisement

Wannan ya kunshi hanyoyin karkashin ƙasa guda uku a yankin Jabalia, inda suka kashe gomman mayaka, a cewar dakarun Isra’ilar.

Sai dai BBC ba ta iya tabbatar da wannan iƙirari na dakarun tsaron Isra’ilar ba nan take.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending