News
Za ma tursasa wa INEC ta ɗora sakamakon zaɓe a yanar gizo – Majalisar Dattawa
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Kwamitin majalisar dattawa mai kula da al’amuran zaɓe ya ce zai tursasa wa hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa, INEC ta riƙa shigar da sakamakon zabe a yanar gizo.
Shugaban kwamitin, Sanata Sharafadeen Alli, ya shaida wa gidan talabijin na Channels a ranar Talata cewa, dokar da ake bi a yanzu ba ta tilasta wa INEC shigar da sakamakon zabe a kan intanet ba, amma kwamitin na ƙoƙarin gyara dokar.
Baya ga sauran sauye-sauyen da ake yi na gudanar da zabe, Alli ya ce kwamitin ya bayar da shawarar warware duk wasu rikita-rikitar tsayar da ƴan takara kafin zabe da tare kuma da inganta fasahar da ake amfani da ita lokacin zabe, sai kuma magance matsalolin da aka samu a baya na amfani da fasaha a zabuka.
A wani labarin kuma Rikicin Siyasar Jihar Ondo Na Kara Daukar Sabon Salo
Kamfanin dillancin labaran Falasɗinawa, WAFA ta rawaito mutane 17 ne suka mutu a hari ta sama da sojin Isra’ila suka kai da tsakar dare, a sansanin ‘yan gudun hijira na Nuseirat da ke tsakiyar Gaza.
Kawo yanzu Isra’ila ba ta ce uffan kan wannan ba.
Ana zargin sojin Isra’ila da kaddamar da hare-hare ta sama babu kakkautawa a asibitocin da ke Gaza.
Sai dai Isra’ila ta kare matakin da cewa ta maida martani ne kan harbin da wani dan bindiga ya yi musu daga wani gini kusa da sansanin ‘yan gudun hijirar.
