News
Yan Kungiyar Asiri 27 Sun Shiga Hannu A Jihar Nasarawa
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Hukumar Tsaron ta Farin Kaya (NSCDC), ta kama wasu mutane 27 kan zargin su da zama mambobin kungiyoyin asiri a Jihar Nasarawa.
Da yake gabatar da wadanda ake zargin, Kwamandan NSCDC na jihar, Bappa Abbas Muhammed, ya ce an kashe wani mutum daya aka kuma sassari wasu da dama da adduna a rikicin kungiyoyin asiri.
Za ma tursasa wa INEC ta ɗora sakamakon zaɓe a yanar gizo – Majalisar Dattawa
Kwamandan na NSCDC ya du za a gurfanar da duk wadana suka shiga hannun a gaban kotu domin su girbi abin da suka shuka.
Da yake bayyana takaicinsa kan abin da ya faru, jami’in ya bayyana damuwa kan karuwar ayyukan kungiyoyin asiri a kananan hukumomi 13 da ke fadin jihar, musamman Lafiya, hedikwatar jihar.
Aminiya ta ruwaito cewa hukumar ta kaddamar da wani sabon aiki na musamman domin shawo kan matsalar.
A wani labarin kuma Za ma tursasa wa INEC ta ɗora sakamakon zaɓe a yanar gizo – Majalisar Dattawa
Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ba da cikakken bayani kan jariran da aka kwashe daga asibitin Al-Shifa na Gaza a karshen mako zuwa Masar.
Jarirai 33 ake kula da su a asibitin Al-Shifa da sojojin Isra’ila suka kai wa samame.
Da yake magana da manema labarai a Geneva, kakakin hukumar ta WHO Christian Lindmeier ya ce jarirai biyu sun mutu kafin a fara kwashe su a ranar Lahadi.
Ya ce hakan ya faru ne saboda rashin kula da su.
Hukumar dai ta ce dukkan jariran da aka kwashe suna “fama da kuma yaƙi da cututtuka masu tsanani kuma suna ci gaba da bukatar kula da lafiyarsu”.
Daga cikin jarirai 31 da aka kwashe daga asibitin Al-Shifa, an kai 28 zuwa Masar.
