Connect with us

News

Idan Za’a Sake Zaben Zamfara Sau 100 Sai Na Lashe — Gwamna Dauda

Published

on

Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

 

Advertisement

Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana kwarin gwiwarsa na cewa ba ya tsoron a sake zaben gwamna, inda ya ce ya shiga takara ne da cikakkiyar kwarin gwiwa.

Gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi ga dimbin magoya bayansa a sakatariyar jam’iyyar PDP ta jihar da ke Gusau, babban birnin jihar a lokacin da ya dawo daga ziyarar da ya kai kasar waje.

Advertisement

An Gudanar Da Jana’izar Mutanen Da Suka Mutu Sanadiyar Hatsarin Kwale-Kwale A Shiroro 

 

Dauda Lawal yace ina da kwarin gwiwar cewa ko da za a yi zabe sau 100 ko shakka babu zan tsira da gagarumin rinjaye.

Advertisement

“Mun yi farin ciki da hukuncin kotun kuma a shirye muke mu shiga takara tare da jam’iyyar, APC, dan takarar gwamna a jihar sa,” in ji shi.

Ya ce Allah ya riga ya yi shi a matsayin Gwamnan Jihar Zamfara, inda ya ba da tabbacin cewa za ta kasance a haka, ko me ‘yan adawa na APC da sauran munafukai za su yi.

Advertisement

Mun fara da kyau, ta hanyar biyan duk wani hakki ga ma’aikatan gwamnati, da biyan kudin jarabawar WAEC da NECO wanda gwamnatin da ta gabata ta ki yi.

A wani labarin kuma An Gudanar Da Jana’izar Mutanen Da Suka Mutu Sanadiyar Hatsarin Kwale-Kwale A Shiroro 

Advertisement

Akalla mutum goma ne suka sannan ashirin suka jikkata lokacin da wata mota ta afka cikin dandazon mutane da suke murnar lashe zaɓen shugaban Laberiya, Joseph Boakai a Monrovia, babban birnin ƙasar.

Wani shafin intanet mai zaman kansa mai suna (Front page Africa website) ya ce hatsarin ya faru ne da yammacin ranar Litinin a hedkwatar jam’iyyar Boakai ta Unity, inda magoya bayansa suka taru don yin murna.

Advertisement

A cewar rahotanni, shaidu sun bayyana cewa direban motar ya buɗe dukkan kofofin motar kafin ya afka cikin mutane.

Hukumar zaɓen ƙasar ta Laberiya ta bayyana Boakai a matsayin wanda yayi nasara a zaɓen shugaban ƙasar zagaye na biyu na ranar 14 ga watan Nuwamba, inda ya kayar da shugaba George Weah kafin a kammala kirag kuri’u.

Advertisement

Boakai,mai shekara 78, ya kasance tsohon mataimakin shugaban ƙasa wanda yayi rashin nasara a hannun weah a zaɓen 2017.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending