News
An Gudanar Da Jana’izar Mutanen Da Suka Mutu Sanadiyar Hatsarin Kwale-Kwale A Shiroro
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Jihar Neja ta gudanar da jana’izar mutane 10 da hatsarin kwale-kwale ya rutsa da su a ranar Alhamis din da ta gabata kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
Cikin wadanda abin ya shafa har da yara takwas.
Zarge-zargen Atiku da PDP kan shari’o’in zaɓe shati-faɗi ne – Fadar shugaban ƙasa
Hotunan da Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja ta fitar a ranar Litinin, sun nuna cewa an binne yaran ne a wani babban kabari mai girma.
Idan dai za a iya tunawa, mutane 34 ne da suka hada da kananan yara 10 na cikin kwale-kwalen wanda ya kife a yayin da suke tafiya a karamar hukumar Shiroro a ranar Alhamis din makon jiya.
Da yake karin haske a ranar Litinin, Daraktan hukumar bauarbAgaji NSEMA, Salihu Garba ya ce binciken da aka gudanar ya nuna cewa, kadawar igiyar ruwa mai karfi da kuma bishiyoyi ne suka haddasa kifewar jirgin.
A wani labarin kuma Zarge-zargen Atiku da PDP kan shari’o’in zaɓe shati-faɗi ne – Fadar shugaban ƙasa
Shugaban ƙungiyar Hamas, Ismail Haniyeh, ya ce su na dab da cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da Isra’ila.
A wata sanarwa da ya wallafa a shafin Telegram, Haniyeh ya ce Hamas ta aika wa Qatar sako wadda ke ƙoƙarin shiga tsakani a tattaunawar kan sako ƙarin waɗanda Hamas ta yi garkuwa da su daga kudancin Isra’ila.
Majiyar masu shiga tsakanin sun ce wannan karon akwai kwarin gwiwa kan batun, za a kuma sako wasu daga cikin waɗanda aka yi garkuwa da su, inda ita kuma Isra’ila za ta dakatar da wuta na kwanaki uku zuwa biyar.
Tuni shugabar ƙungiyar agaji ta Red Cross ta tafi Qatar domin tattauna batun sakin Isra’ilawan.
