Connect with us

News

SEMA: Akalla gidaje 700 da gonaki 700 ne ambaliyar ruwa ta lalata a Bauchi

Published

on

Ambaliyar ruwa

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN

 

Advertisement

Akalla gidaje 700 da gonaki 700 ne ambaliyar ruwa ta lalata a yankin Cheledi da ke karamar hukumar Kirfi ta jihar Bauchi.

Adamu Nayola, daraktan tsare-tsare, bincike da kididdiga a hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar (SEMA), ya bayyanawa Kamfani dillancin labarai na kasa NAN a ranar Litinin.

Advertisement

Rundunar soji ta kama masu laifukan kisa, garkuwa da mutane, da kuma fashi da makami 17 a jihohi 3

Nayola ya ce gidaje da gonaki da abin ya shafa sun lalace ne a lokacin da kogunan yankin ya cika bayan ruwan sama kamar da bakin kwarya.

Sama da gidaje da filayen noma 700 ne suka lalace a yankin Cheledi tare da lalata gona kin shinkafa, masara, dawa, gero, dadai sauran su

Advertisement

Ya bayyana lamarin a matsayin mai muni kuma mafi muni da ya faru a jihar a bana, inda ya kara da cewa ambaliyar ta sa mazauna unguwar da dama suka rasa matsuguni.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending