Connect with us

News

Gamayyar Kungiyaar CODDAE Ta Kudiri Aniyar Maka Najeriya A Kotu

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

Advertisement

Kungiyoyin kare hakkin jama’a a fannin makamashi mambobin gamayyar CODDAE A Jmhuriyar Nijer sun kudiri aniyar shigar da kara a gaban kotu saboda zargin Najeriya da yin fatali da yarjejeniyar kasuwancin da ke tsakaninta da Nijer a fannin makamashi.

Najeriya ce ke bai wa Nijer Kashi 70 daga cikin 100 na wutar lantarkin da jama’ar kasar ke bukata sai dai gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta katse wutar a wani bangare na takunkumin kungiyar CEDEAO biyo bayan juyin mulkin 26 ga watan Yulin 2023, matakin da ‘yan fafutika suka ce ya saba wa doka dalili kenan suka kudiri aniyar garzayawa kotu kamar yadda jagoransu Alhaji Moustapha Kadi ya bayyana a taron manema labaran da suka kira.

Advertisement

Kotun Kasar Faransa ta amince a haramta wa dalibai sanya abaya

Muryar amurka ta rawaito cewa Alhaji Moustapha yace ya zama wajibi jama’ar kasa da na duniya baki daya su sani duk da yake shugaba Bola Ahmed Tinubu na da ‘yancin katse wutar da kasarsa ke ba Nijer to amma matakin ya saba wa yarjejeniyar da ta shimfida wannan haraka sabili kenan gamayyar CODDAE ta lashi takobin kai koke a gaban kotu domin ta kwato wa ‘yan Nijer hakkinsu sai dai kawo yanzu ba su saka ranar shigar da karar ba.

Matakin na Tarayyar Najeriya ya haddasa tsayawar al’amura a fannoni da dama inda ‘yan Nijer ke tafka asarar dimbin kudade a kowace rana alhali tun kafin a girka ECOWAS kasashen biyu suka kulla yarjejeniyar kasuwancin wutar lantarki.

Advertisement

Kotun Kasar Faransa ta amince a haramta wa dalibai sanya abaya

Rashin wutar lantarki da ake fama dashi tun kafin yanzu ya kara tsananta jiya a nan Jihar Kano, A yayin da kanfanin rarraba hasken wutar lantarki na KEDCO ya tsayar da aiyukansa kacokan, Lamarin da ya haifar da daukewar lantarki baki daya a cikin birnin Kano.

Advertisement

 

Wata sanarwa da shugaban sashin sadarwar kanfanin, Sani Bala Sani ya fitar, Ya alakanta daukewar wutar lantarkin da yin biyayya ga umarnin kungiyar kwadago ta kasa na tafiya yajin aikin gargadi na tsawon kwanaki biyu.

Advertisement

 

Sanarwar da aka wallafa a shafin X na kanfanin, Ta baiyana cewar za’a cigaba da fuskantar matsalar daukewar wutar lantarkin, kasancewar yajin aikin gargadin zai ci gaba da kasancewa a yau Laraba.

Advertisement

Shima mataimakin shugaban kungiyar kwadago ta kasa reshen jihar Kano, Kwamared Ado Riruwai, ya tabbatar da cewar kungiyarsu ta rufe dukkanin wasu ofisoshin gwamnati dake jihar Kano, domin tabbatar da yajin aikin gargadin.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending