Connect with us

News

Gwamnatin Tarayya Tace Watan Gobe Za’a Fara Rabawa Talakawa Naira Dubu 25

Published

on

Ministar bada tallafi da kawar da fatara Betta Edu

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

 

Shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da biyan naira dubu 25 a kowane wata ga masu karamin karfi dake cikin rijistar bada tallafin tsabar kudi na gwamnatin tarayya.

Ministar bada tallafi da kawar da fatara Betta Edu ce ta sanar da haka a ranar Alhamis, Inda ta ce shugaban kasar ya umarci ma’aikatar data fara biyan kudin daga watan gobe.

Rukunin farko na dakarun Faransa sun fara ficewa daga Jamhuriyar Nijar

Sanarwar da mashawarcinta a bangaren yada labarai Rasheed Zubair ya fitar, Ta Ambato ministan na baiyana haka a lokacin da take ganawa da shugaban kungiyar kwadago ta kasa NLC Joe Ajeoro da kuma takwaransa na TUC Festus Osifo a Abuja.

Ta yi kira ga kungiyoyin kwadagon dasu temakawa yunkurin gwamnati wajen gaggauta tattara bayanan masu karamin karfi a kasar nan, domin fara cin gajiyar tsarin.

Advertisement

A Wani labarin kuma Rukunin farko na dakarun Faransa sun fara ficewa daga Jamhuriyar Nijar

Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.

Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.

A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.

Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending