News
Gwamnatin tarayya za ta kaddamar da shirin bayar da tallafin kudi ga gidaje miliyan 15 a mako mai zuwa -Betta Edu
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Ministar harkokin jin kai da rage radadin talauci Betta Edu ta ce gwamnatin tarayya za ta kaddamar da shirin bayar da tallafin kudi ga gidaje miliyan 15 a mako mai zuwa ranar Talata 17 ga watan Oktoba na bana.
Edu ta tabbatar da haka a daren jiya ta cikin wani shirin gidan talabijin, watanni bayan gwamnatin tarayya ta dakatar da biyan tallafin man fetur.
Dalilin Da Ya Sa A Yanzu Buhari Yake Rayuwar Nadama — Solomon Dalung
Ministar ta ce ana saran samun amincewa daga shugaban kasa kan shirin a cikin wannan mako da kuma kaddamar da shirin a hukumance a mako mai zuwa.
A cewarta, ma’aikatar tana aiki tare da masu ruwa da tsaki a fadin kasarnan domin samun rijista mai sahihanci ta wadanda za su amfana domin tabbatar da cewa wadanda ke cikin rijistar ‘yan Najeriya ne da ke samun abunda ya gaza dala 1.95 a kowacce rana.
A wani labarin kuma Dalilin Da Ya Sa A Yanzu Buhari Yake Rayuwar Nadama — Solomon Dalung
Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.
Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.
A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.
Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.
