News
Majalisar Wakilan Kassr nan Zata Raba Sabbin Motoci Ga ‘Yan Majalisar

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Majalisar Wakilai ta ce ta kammala shirye-shiryen da suka dace domin raba sabbin motoci ga ‘yan majalisar nan da cikin makonni masu zuwa.
Mai magana da Yawun zauren Majalisar, Akin Rotimi, shi ne ya tabbatar da da haka ta cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, inda ya ce ‘yan Najeriya sun cancanci sanin halin da ake ciki, kasancewar za’a rika yiwa labarin karin gishiri a shafukan sada zumunta.
Rotimi ya bayyana cewa motocin da za a raba wa ofisoshin Yan majalisar , motoci ne da aka samar dasu domin gudanar da ayyukansu na sa ido, ba wai motocin su bane na kashin kai.
Ya kara da cewa ‘yan majalisar na iya mallakar motocin, ta hanyar biyan kudin motar a Aljihun gwamnati, kafin su zama mallakinsu , idan wa’adinsu ya kare a shekarar 2027, Amma idan ba haka ba sun zama mallakin Majalisar Dokoki ta kasa.
A wani labarin kuma Rundunar sojin sama Sun Halaka Mayakan ISWAP Kimanin 100
Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.
Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.
A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.
Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.
