News
Tinubu Zai Gabatar Da Kasafin Kudin Na 2024 A Watan Nuwamba
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu zai gabatar da kasafin kudin 2024 ga majalisar dokokin kasar nan a cikin watan Nuwamba dake tafe.
Ana kuma saran shugaban kasar ya mika kwarya-kwaryan kasafin kudin shekarar 2023 ga majalisar dokokin kasar nan domin nazari da tantancewa da kuma amincewa.
Gwamnatin Tarraya Na Barazanar Daina Biyan Albashi Ga Ma’aikatan Da Suka Bijirewa Rijista Da IPPIS
Shugaban Kwamitin Kasafin Kudi na Majalisar Dattawa, Solomon Adeola, wanda ya bayyana hakan a yayin taron kaddamar da kwamitin a ranar Laraba, ya bayyana cewa majalisar za ta tabbatar da cewa an zartar da kasafin kudin 2024 akan lokacin da ya dace.
Hakan na zuwa ne lokacin da Ministan kasafin kudi da tsare-tsaren tattalin arziki, Atiku Bagudu, ya ce Najeriya ta zama dandali na masu zuba jari daga kasashen waje don cin gajiyar abubuwa da dama.
Ministan ya bayyana haka ne a karshen taron tattalin arzikin Najeriya na 2023 a Abuja.
Bagudu ya ce duk da kalubalen da kasar nan ke fuskanta, gwamnati ta ci gaba da jajircewa, kuma tana ci gaba da gudanar da ayyukan tattalin arziki a dukkan sassan kasar nan.
A wani labarin kuma Gwamnatin Tarraya Na Barazanar Daina Biyan Albashi Ga Ma’aikatan Da Suka Bijirewa Rijista Da IPPIS
Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.
Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.l
A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.
Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.
-
Opinion4 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News6 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News3 days ago
Gwamna Abba Ya Ayyana Murtala Sule Garo A Matsayin Wanda Zai Yi Masa Takarar Mataimakin Gwamna A Zaɓen 2027
