News
Ana zargin wani matashi da kisan karamin yaro tare ƙwaƙwule masa Idanu a Kano
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Ana zargin wani matashi da kisan karamin yaro tare ƙwaƙwule masa Idanu a Kano
Nassara Radio ta rawaito cewa Lamarin ya faru ne da safiyar ranar Lahadi Unguwar Dandago dake birnin Kano.
An zargi matashi mai suna Dan Umma da hallaka wani yaro dan shekara biyar mai suna Muhammad Suyudi, ta hanyar yi masa yankan rago tare da ƙwaƙwule masa idonu.
Jami’an yan sanda sun tafi da matashin wanda ake zargin mutanen Unguwa sun dauki doka a hannunsu, ta hanyar sassara shi bayan sun same shi da gawar yaron, wanda shima yanzu haka yana kwance a Asibiti, kamar yadda mai Unguwar Dandago, Malam Muhammad Sani ya tabbatar.
Sai dai kuma dan uwan matashin mai suna Shazali, yace ƙanin nasa yana fama da lalurar kwakwalwa, ya kwanta a Asibitin Dawanau a ƙalla sau bakwai, yanzu ma bai dade da fitowa ba, kasancewar lalurar tasa motsi-motsi ce, a haka ba lallai a gane cewa bashi da lafiya ba sai idan ta motsa, amma dukda haka, Shazali yace a madadin danginsu, suna bada hakuri.
A wani labarin kuma Ana Harbe-Harbe A Jahar Ribas Bayan Majalisar Jihar Ta Fara Shirin Tsige Gwama
Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.
Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.
A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.
Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
