News
zaben Gwamnan Kano :Alkalai suna hukunta masu kada kuri’a kan kurakuran da INEC -Femi Falana
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Babban lauyan kare hakkin bil’adama a Nageriya, Femi Falana, ya caccaki hukuncin da kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan Kano ta yanke wanda ya soke nasarar Gwamna Abba Kabir Yusuf.
Jaridar Inda Ranka ta rawaito cewa hukumar zabe Mai zaman kanata ta kasa INEC, ta ayyana Gwamna Yusuf bisa cancanta a zaben gwamna da aka gudanar a jihar a ranar 18 ga Maris, 2023.
Rwanda Ta Bada Sanarwar Shiga Kasar Ba Tare da Biza Ba Ga ‘Yan Afirka
Da yake magana a shirin Sunrise na Channels TV a ranar Juma’a, Falana ya ce, “Ba za ku iya hukunta masu kada kuri’a kan kura-kuran da INEC ta yi ba, abin da ya faru a Kano kwanan nan ke nan, inda aka ce kuri’u 65,000 da jami’an INEC ba su samu ba.
Ya kara da cewa: “Muna rokon alkalan mu da su rungumi adalci,ta yadda ba za ku iya hukunta masu kada kuri’a kan kurakuran da INEC ta yi ba”.
A cewar jiga-jigan shari’a, da zarar an kidaya kuri’u kuma aka bayyana wanda ya yi nasara, “Ba za ka iya kalubalantar ingancin katin zabe ba”.
“Don haka ina ganin wadannan su ne wuraren da alkalan mu za su koma kan teburin adallci.
A wani labarin kuma Rwanda Ta Bada Sanarwar Shiga Kasar Ba Tare da Biza Ba Ga ‘Yan Afirka
Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.
Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.
A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.
Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
