Connect with us

Business

Duk Wadanda Muke Bi Bashi Sai Sun Biya —Kamfanin MTN

Published

on

 

Kamfanin Sadarwa na MTN ya sha alwashin cewa duk wasu abokanan huldarsa da yake bi bashi su kwana da sanin cewa sai sun biya.

Kamfanin ya bayyana hakan yayin da aka wayi gari yau Asabar musamman a dandalan sada zumunta cewa ya yafe wa abokanan huldarsa basussukan da suka ci.

Babbar Magana: An Kame Dan Takarar Gwamna A Jahar Kogi 

A cewar kamfanin na MTN, tangardar na’ura ya fuskanta wadda ta yi kuskuren goge basussukan abokanan huldarsa, kuma da zarar ya yi wa tufkar hanci bayanan bashin za su dawo.

 

Ya bayyana cewa matsalar na’urar da ya fuskanta ce ta sanya aka rika ganin ba daidai ba wajen neman ganin ragowar kudade da data na abokanan huldarsa.

Advertisement

 

MTN ya ce wannan dalili shi ya taka rawar da abokanan huldarsa suka rika ganin babu basussukan da ake binsu.

Daily Trust ta ruwaito cewa, dandalan sada zumunta sun rikide da farin ciki a yayin da masu amfani da layin sadarwa na MTN suka yi tsammanin an sauke musu nauyin basussukan da kamfanin ke binsu.

 

Wannan lamari dai ya zo ne bagatatan ba tare da wata sanarwa daga kamfanin sadarwar ba.

 

Advertisement

Sai dai a cikin wata sanarwa da kamfanin ya fitar a Yammacin wannan Asabar din, ya ce dole murna ta koma ciki domin kuwa tangardar na’ura ya fuskanta, yana mai cewa da zarar komai ya daidaita hakikanin bayanan da abokanan huldarsa suka buƙata dangane da kuɗin da ke layinsu za su bayyana babu ragi ko kari.

 

 

Saboda haka kamfanin ya ce duk wadanda yake bi bashi za su ga hakikanin bashin da ake binsu da zarar injiniyoyinsu sun kammala gyare-gyare.

 

Da wannan sanarwa kuma kamfanin yake bai wa abokanan huldarsa hakuri kan duk wani yanayi da matsalar ta jefa su a ciki.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending