Connect with us

News

Wata gobara ta tashi a babbar kasuwar Gamboru da ke Maiduguri

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

 

Wata gobara ta tashi a babbar kasuwar Gamboru da ke Maiduguri babban birnin jihar Borno da sanyin safiyar Lahadi.

Daily Post ta rawaito cewa Har yanzu dai ba a gano musabbabin barkewar gobarar ba. Rahotanni sun ce an dauki kokarin kungiyoyin ‘yan banga da suka hada da Civilian JTF da mazauna yankin wajen kashe wutar.

Hukumar Hizbah Ta Jihar Yobe Ta Kama Bata Garin ‘Yan Mata Da Masu Sayar Barasa A wasu sassan dake Jihar.

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Borno, SEMA, ta tabbatar da faruwar lamarin a shafinta na Facebook a lokacin da babban daraktan hukumar Dr Barkindo Muhammad Saidu ya ziyarci inda lamarin ya faru a safiyar yau.

“Gobarar da ta tashi da sanyin safiyar ranar Lahadi 12/11/2023 ta kone shaguna, duk da cewa ba a tantance hasarar rayuka ba,” in ji hukumar.

Advertisement

Gobarar dai ta zo ne watanni tara bayan da gobarar ta tashi a babbar kasuwar Litinin ta Maiduguri, inda ta lalata shaguna da kayayyaki na biliyoyin Naira.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending