News
Gobara ta kone sansanin ‘yan gudun hijira a jihar Borno
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
An samu a sarar dukiyoyi da wasu kayayyaki masu daraja a wata gobara da ta tashi a wani sansanin ‘yan gudun hijira da ke Muna a karamar hukumar Jere a jihar Borno.
Jaridar Daily Post ta ruwaito cewa gobarar ta tashi ne da sanyin safiyar Laraba.
Mutane 4 sun mutu yayin daa wata babbar mota dauke da kwantena ta murkushe Motoci uku
Jami’an Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Borno (SEMA), sun kai ziyarar tantance wuraren da lamarin ya faru.
Har zuwa lokacin cika wannan rahoto, ba a tantance musabbabin tashin gobarar ba.
Wannan na zuwa ne kwanaki kadan bayan wata gobara ta kone shaguna da dukiyoyi na miliyoyin Naira a babbar kasuwar Gamboru da ke Maiduguri babban birnin jihar Borno.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
