News
Majalisar wakilai Za ta Karfafawa Hukumomin Tsaro don Tunkarar Kalubalen Tsaro — Abbas
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Kakakin Majalisar Wakilai Tajudeen Abbas ya ce majalisa ta 10 za ta yi kokarin karfafa rundunar sojojin Najeriya da sauran hukumomin tsaro domin tunkarar kalubalen tsaro a Najeriya
Kakakin majalisar ya bayyana hakan ne a wani taron kwanaki biyu bayan rantsar da mambobin kwamitin tsaro na majalisar
Majalisa wakilai ta 10 za ta ci gaba da tallafawa kokarin hukumomin tsaro ta hanyar samar isassun kudade, samar da kayan aiki na zamani da sauransu
Kakakin Majalisar Wakilai Tajudeen Abbas ya ce majalisa ta 10 za ta yi kokarin karfafa rundunar sojojin Najeriya da sauran hukumomin tsaro domin tunkarar kalubalen tsaro a kasar.
Abbas, wanda ya bayyana hakan a wani taron kwanaki biyu bayan rantsar da mambobin kwamitin tsaro na majalisar, ya yi kira da a hada karfi da karfe domin tunkarar kalubalen tsaro masu sarkakiya a kasar.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Mista Musa Krishi, babban mai baiwa shugaban majalisar shawara kan harkokin yada labarai da wayar da kan jama’a ya fitar a Abuja ranar Asabar.
Ya bayar da shawarar samar da cikakken tsarin tsaro na kasa, inda ya kara da cewa akwai bukatar a kara karfin rundunar soji da sauran hukumomin tsaro.
Abbas ya ce majalisar wakilai ta 10 za ta ci gaba da tallafawa kokarin hukumomin tsaro ta hanyar samar da isassun kudade, samar da kayan aiki na zamani, horaswa da inganta jin dadin jami’an tsaro.
A wani labarin kuma Gwamnatin Tarayya Za Ta Kirkiro Hukumar Kula Da Filaye
Rahotonni na cewa an kai wa wata makarantar Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) hari a arewacin Birnin Gaza, inda aka kashe mutane da dama tare da jikkata wasu.
Ma’aikatar lafiya da ke Zirin Gaza ta faɗa wa kamfanin labarai na AFP cewa an kashe aƙalla mutum 50 sakamakon harin da Isra’ila ta kai kan makarantar ta Al-Fakhoura da ke cikin sansanin Jabalia.
Sai dai rundunar sojin Isra’ila ta ce tana bincike kan lamarin.
BBC ba ta iya tabbatar da abin da ya faru ba, amma mun ga wani sahihin bidiyo da ke nuna mutane da yawa da aka ji wa rauni a wurin.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
