Connect with us

News

Boko Haram Sun Raunata Jami’an Tsaron Gwamnan  Jihar Yobe 6

Published

on

Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN

 

Akalla jami’an tsaron gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni shida ne suka samu rauni yayin wani harin da ‘yan ta’addar Boko Haram suka kai musu a hanyar Maiduguri zuwa Damaturu.

Gwamna Buni yana Maiduguri tare da manyan baki domin halartar taro karo na 24 a Jami’ar Maiduguri (UNIMAID) lokacin da lamarin ya faru.

SIYASAR Kano: Kotun daukaka kara ta yanke hukunci na wucin gadi ne – Jigon NNPP

Gwamnan da ‘yan tawagarsa wadanda suka samu rakiyar gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, sun tafi Abuja a jirgin sama ta sansanin sojin sama da ke Maiduguri.

Leadership ta ruwaito cewa Majiyoyin leken asiri sun bayyana wa Zagazola Makama, wani kwararre kan yaki da tada kayar baya kuma mai sharhi kan harkokin tsaro a yankin tafkin Chadi, cewa motocin jami’an tsaron da ke cikin ayarin gwamnan, ‘yan ta’addar sun farmake su a babbar hanyar Jakana.

Advertisement

Majiyar ta ce ‘yan ta’addar sun harbe sojojin da ke jagorantar ayarin motocin MRAP da wata motar bindigu da kuma wata motar da ke jigilar ‘yan sanda da jami’an DSS.

“Sai dai sojojin sun mayar da martani ta hanyar bude wuta, lamarin da ya tilasta wa ‘yan ta’addar tserewa, abin takaici, sojoji biyu da suka hada da direba daya da ‘yansanda hudu sun samu raunuka.

“Jami’an tsaro sun dawo Yobe lafiya, yayin da aka kai wadanda suka jikkata asibiti domin kula da lafiyarsu,” in ji Makama.

A wani labarin kuma SIYASAR Kano: Kotun daukaka kara ta yanke hukunci na wucin gadi ne – Jigon NNPP

Ɗazun nan muka bayar da rahoton harin da aka kai wa wata makarantar MDD a sansanin Jabalia da ke arewacin Gaza, wanda ma’aikatar lafiya a Gaza ta ce ya kashe mutum 50.

Tun daga lokacin ne kuma rundunar sojin Isra’ila ta fara bayyana yadda “za ta faɗaɗa hare-haren da take kaiwa” a sassan zirin na Falasɗinawa.

Advertisement

Rundunar da ake yi wa laƙabi da IDF ta ce a cikin awa 24 da suka wuce “ta kai hare-hare a Zaytun da sansanin Jabalia, inda suka yi arangama da ‘yan ta’adda da suka kai mata hari daga gidajen farar hula da makaman harbe tanka da bama-bamai”.

Ta ƙara da cewa dakarunta sun “kashe” adadi mai yawa na mayaƙan Hamas, “kuma ta hari gine-ginen ‘yan ta’adda da dama”.

Kafin yanzu, mai magana da yawun IDF, Laftanar Kanar Peter Lerner, ya faɗa wa BBC cewa suna bincike kan harin.

 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending