News
An Gano Gawarwaki 9 Bayan Hatsarin Kwale-Kwale A Shiroro
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Neja, NSEMA, ta ce an gano gawarwaki 9 a wani hatsarin kwale-kwale da ya afku a karamar hukumar Shiroro da ke jihar.
Shugaban hukumar NSEMA, Alhaji Salihu Garba ne ya bayyana hakan a wata zantawa da kamfanin dillancin labaru na kasa NAN a Minna ranar Lahadi.
Kungiyar Direbobin Tankar Dakon Fetur Na Barazanar Ballewa Daga Kungiyar NUPENG
Idan za’a iya tunawa, Rahoton NAN yace an tabbatar da mutuwar mutane goma a wani hatsarin kwale-kwale da ya afku a ranar Alhamis, 16 ga watan Nuwamba.
Rahotanni sun bayyana cewa wadanda al’amarin ya rutsa da su, ‘yan kasuwa ne, suna jigilar kaya ne daga unguwar Zongoru da ke gundumar Bassa zuwa Gijiwa, gabanin kasuwar Juma’a da ke Kuta, shalkwatar karamar hukumar Shiroro, a lokacin da al’amarin ya faru.
A wani labarin kuma Kungiyar Direbobin Tankar Dakon Fetur Na Barazanar Ballewa Daga Kungiyar NUPENG
Gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang, ya bayyana hukuncin da kotun ɗaukaka ƙara ta yanke na soke zaɓensa a matsayin koma baya na wucin-gadi, wanda ba zai hana shi mayar da jihar kan turbar hadin kai da zaman lafiya da ci gaba ba.
Ya kuma bayyana ƙwarin gwiwar cewa za a dawo da nasarar da al’ummar jihar suka ba shi, domin ya umurci tawagarsa ta lauyoyi su shigar da ƙara a kotun ƙoli.
Mutfwang, a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, ya buƙaci al’ummar jihar da magoya bayan jam’iyyar PDP da su kwantar da hankalinsu, ya kuma ba su tabbacin za a martaba da kare zaɓin al’umma.
Ya kara jaddada aniyarsa ta bin doka da oda, ya kuma tabbatar wa jama’a cewa za a cimma haske a karshe, domin ya yi imani da adalcin ɓangaren shari’a da kuma kundin tsarin mulkin Najeriya.
Mutfwang ya buƙaci magoya bayansa, da kuma ‘yan jihar da su tabbatar da doka da oda.
Ya kuma tabbatar da cewa jihar za ta yi nasara inda ya sake tabbatar da aniyarsa ta ci gaba da yi wa jihar hidima da kwazo da gaskiya.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
