Connect with us

News

Joe Biden Ya Ce An Kusa ƙulla Yarjejeniya tsakanin Isra’ila da Hamas

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN

 

Shugaban Amurka Joe Biden ya nuna cewa nan gaba kaɗan za a ƙulla yarjejeniyar da za ta kai ga sakin mutanen da mayaƙan da Hamas ke garkuwa da su a Zirin Gaza.

Rahotonni sun ce Hamas za ta saki wasu daga cikin mutanen a madadin tsagaita wuta na wasu ‘yan kwanaki da Isra’ila za ta yi a hare-haren da take kaiwa a zirin.

Har Yanzu Akwai Gibin Shinkafa Sama Da Tan Milliyan 2 A Najeriya – Bincike

Biden ya yi kalaman ne yayin taron cikaciki na shekara-shekara.

Da wani ɗan jarida ya tambaye shi game da yarjejeniyar da aka ce an kusa ƙullawa, Biden ya bayar da amsa da cewa: “Ina ganin haka”.

Advertisement

A ranar Lahadi, jaridar Washington Post ta ruwaito cewa an kusa ƙulla yarjejeniyar, kuma jakadan Isra’ila a Amurka ya faɗa ranar Lahadi cewa yana da ƙwarin gwiwar za a cimma yarjejeniyar “cikin ‘yan kwanaki masu zuwa”.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending