News
Gobe Talata Kotun Daukaka Kara Zata Raba Gardama A Adamawa
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Kotun daukaka kara da ke zamanta a Abuja, ta sanar da gobe Talata, a matsayin ranar da zata yanke hukunci tsakanin Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri da dan takarar kujerar gwamna a jam’iyyar SDP a zaben 2023, Dakta Umar Ardo.
Dakta Umar Ardo, na kalubalantar nasarar da Kotun sauraron kararrakin zabe ta yanke wacce ta tabbatar da hukuncin INEC na ayyana Gwamna Ahmadu Fintiri a matsayin Gwamnan Jihar Adamawa.
Kiri-ƙiri alƙalai suke yi wa APC aiki a shari’o’in zaben Najeriya – Atiku Abubakar
Haka kuma Dakta Umar Ardo, ya nemi Kotun da ta rushe hukuncin da Kotun sauraron kararrakin zaben ta yanke tun a farko.
A wani labarin kuma Kiri-ƙiri alƙalai suke yi wa APC aiki a shari’o’in zaben Najeriya – Atiku Abubakar
An yanke wa fiye da mutum 200 hukuncin zaman gidan yari na jimillar shekara 2,200, a daya daga cikin shari’o’in ‘yan mafiyan kasar Italiya mafi girma.
Shari’ar ta tsawon shekara uku ta kai ga yanke wa wasu daidaikun mutane da ake zargin suna da alaka da ‘Ndrangheta, hukunci kan laifukan da suka shafi kwace da kuma safarar miyagun kwayoyi.
Daga cikin wadanda aka yanke wa hukuncin har da wani tsohon sanatan kasar, ko da yake ana iya daukaka kara a kan hukuncin.
‘Ndrangheta na daya daga cikin kungiyoyin aikata laifuka mafi tasiri a nahiyar Turai.
Karar tana nuna faffadan tasirin da kungiyoyin masu aikata laifuka ke da shi a cikin harkokin siyasa da na al’umma a kudancin Italiya.
Kwararru sun ce hukunce-hukuncen kan ma’aikata masu manyan mukamai cikinsu har da jami’an kananan hukumomi da ‘yan kasuwa da ‘yan siyasa, na nuna matukar girman tasirin da kungiyoyin aikata laifuka da shi a harkokin hukumomin Italiya.
Cikin fitattun mutanen da aka yanke wa hukuncin, akwai Giancarlo Pittelli, wanda lauya ne kuma tsohon sanata a zamanin gwamnatin jam’iyyar Forza Italia ta tsohon Firaminista Silvio Berlusconi.
An dai yanke wa Pittelli hukuncin shekara 11 a gidan yari saboda hada baki da wata kungiya irin ta ‘yan mafiya.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News6 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News3 days ago
Gwamna Abba Ya Ayyana Murtala Sule Garo A Matsayin Wanda Zai Yi Masa Takarar Mataimakin Gwamna A Zaɓen 2027
