Connect with us

News

Majalisa Ta Fara Bincike Akan Naira Tiriliyan 12 Da Aka Kashen Wajen Gyaran Matatun Mai

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

Advertisement

Majalisar dattijai a ranar Laraba ta sha alwashin tabbatar da cewa an kori shugaban kamfanin man fetur na kasa (NNPCL), Mele Kyari da wasu manyan jami’an kamfanin tare da gurfanar da su gaban kuliya bisa zargin kashe naira tiriliyan 12 da ake zargin an kashe wajen kula matatun mai na kasa.

Majalisar ta Red Chamber ta bayyana cewa an kashe sama da Naira Tiriliyan 12 kan matatun inda ta ce tana da bayanan sama da dala miliyan 592, da Yuro miliyan 4.8 da kuma fam miliyan 3.4 da aka kashe a tsakanin shekarar 2010 zuwa 2023 kan TAM, amma duk da haka matatun man ba sa aiki.

Advertisement

Hukuncin Da Muka Zartar Na Korar Gwamnan Kano Na Nan Daram – Kotu

Kwamitin wucin gadi na Majalisar Dattawa da ke binciken ayyukan matatun Najeriya daban-daban ne suka yi wannan barazanar a yayin wani zaman tattaunawa da mahukuntan NNPC da sauran shuwagabannin bangaren mai.

Wasu daga cikin hukumomin da aka gayyata, wadanda manya shugabanninsu suka kasa zuwa amma sai suka tura wakilai a maimakon haka, kuma kwamitin ya yi barazanar korarsu tare da daure su, sun hada da NNPCPL, Nigerian Midstream and Downstream Petroleum Regulatory Authority (NMDPRA) da kuma Nigerian Upstream Petroleum Regulatory Commission (NUPRC).

Advertisement

Shugaban kwamitin wucin gadi, Sanata Isa Jibrin (APC, Kogi ta Gabas), ya bayyana cewa an ji abubuwa da yawa game da yunkurin da aka yi na kawo sauyi da kuma kashe makudan kudade wajen samar da kayan aiki na matatun da ba sa aiki..

Mun aika musu gayyata fiye da makonni biyu da suka gabata muna neman takardu kuma ba a fitar da takardun ba bayan makonni biyu. Don haka, muna son shugabannin zartarwa su hallara.

Advertisement

Abin da ya fi daukar hankali shi ne, a tsakanin shekarar 2010 zuwa 2020, an ce an kashe Naira Tiriliyan 4.8 a matsayin kashe kudi na aiki.

Ta yaya kuke biyan kuɗin aiki da ke da alaƙa da siyan kayan albarkatun ƙasa da makamantansu akan masana’anta da suka lalace,muna bukatar mu sani.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending