Connect with us

News

Gobara Ta Tashi A Babbar Kasuwar Kabba Ta Jihar Kogi

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN

 

Gobarar ta kone kayayyakin amfani da kadarori na miliyoyin Naira yayin a gobarar da ta tashi a safiyar ranar Litinin.

Gobarar ta ci shaguna da dama, lamarin da ya jefa ‘yan kasuwa da mazauna yankin cikin damuwa da firgici sakamakon asarar da aka tabka a kasuwar.

Masu Garkuwa Da Mutane 4 Sun Shiga Hannu A Jihar  Jigawa

LEADERSHIP ta rawaito cewa, gobarar ta tashi ne da misalin karfe 5 na safe inda cikin kankanin lokaci ta bazu cikin manyan shagunan kasuwar.

Muyane da dama da suka je wurin sun yi kokarin kashe gobarar da hana ta ci gaba da yaduwa, amma duk da kokarin da suka yi sun gaza kashe wutar.

Advertisement

Wasu da lamarin ya faru kan idonsu sun ce, masu shagunan ba su tsira da komai na kayansu don a kan idonsu suna kallon kayansu na ci da wuta.

 

Yanzu haka ana ci gaba da gudanar da bincike kan musabbabin tashin gobarar, sai dai mutanen yankin na Kabba sun nuna rashin damuwarsu kan rashin kayan aikin kashe gobara a kasuwar da zai taimaka wajen kashe wutar a kan lokaci.

A Wani labarin kuma Masu Garkuwa Da Mutane 4 Sun Shiga Hannu A Jihar  Jigawa

Gawurtacciyar guguwa haɗe da ruwan sama sun auka wa kudancin ƙasar Ukraine, lamarin da aka jima ba a gani ba cikin shekaru a yankin Tekun Baharul Aswad.

Kusan mutum dubu biyar da ke yankin Crimea wanda Rasha ta mamaye na zaune ba tare da wutar lantarki ba, bayan guguwar ta karya manyan bishiyoyin da suka faɗa kan turakun wutar lantarki.

Advertisement

Guguwar ta kuma janyo ambaliyar ruwa a kauyuka da garuruwan da ke kusa, an kuma kwashe mazauna garin Sebastopol bayan ambaliyar da kogin yankin ya yi.

Hotunan da aka yaɗa a intanet sun nuna biranen Bed-yansk da Mariupol da Tekun Azov duk ruwa ya mamaye.

A can yammacin birnin Odesa ma lamarin ya yi muni.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending